Shekaru ashirin da suka shige ne aka kafa hukumar kare hakin bil’adama ta Najeriya, domin bin diddigin duk wani haki da aka tauyewa dan Najeriya ta kowacce fuska da suka hada da biyan albashi da kuma wadansu hakkokinsu.
To sai aka wayi gari suma ma’aikatan wannan hukuma, sun sami kansu a bangaren wadanda suke kokarin karewa, domin kuwa sun shafe watanni biyu ba a biya su albashi ba. Mai Magana da yawun ma’aikatan ya bayyana cewa, komi ya tabarbare a hukumar kare hakkin bil’adaman ta Najeriya, ya kuma zama abin takaici cewa, suna aikin kare hakkokin al’umma amma sub a a kare hakinsu ba.
Ya bayyana cewa, tilas ne su saurari masu kawo koke koke duk da yake babu kayan aiki a ofis din ba a kuma biyansu albashi.
Ma’aikatan hukumar sun yi kira ga ‘yan majalisa da gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike a kuma kawar da duk wadanda suke danne hakkin ma’aikatan.
Baya ga batutuwan da suka shafi batun albashi da kuma hakkokin aiki, ma’aikatan sun kuma koka kan yadda shugabanni suka hana su kafa kungiya da zata rika bin batutuwan da suka shafi sha’anin aiki da jin dadinsu.
Your browser doesn’t support HTML5
Ga cikakken rahoto da Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana daga Kano