Gwamnatin wucingadi na Taraba da ta shude ranar 29 ga watan jiya ta baiwa malaman jami'ar jihar takardar kudi ta bogi.
A wani yunkuri da tayi da ya yi kama da yaudara domin malaman jami'arta su kawo karshen yajin aiki, tsohuwar gwamnatin ta basu takardar kudi ta nera miliyan dari daya. Yajin aikin ya dauki tsawon kwanaki 75.Amma daga bisani an iske cewa babu ko kwandala a cikin asusun baki manlakar gwamnatin jihar.
Dr Reuben Jonathan shugaban kungiyar malaman jami'ar ya tabbatar da wannan yaudara da gwamnatin ta yi masu. Amma yace ashirye suke su koma bakin aiki matukar sabuwar gwamnatin zata mutunta yarjejeniyar da ta yi dasu tare da mayar da gurbin takardar kudin da aka yaudaresu da ita. Yace idan gwamnati ta biysu kudin wancan takardar da aka yaudarsu da ita kuma idan ta yadda ashirye suke su amince da a dinga biyansu sauran kudadensu sannu a hankali. Amma idan basu biya wadannan nema mililyan dai din ba ba zasu koma bakin aiki ba.
Dr Jonathan yace gwamnati da ta shude ta yiwa ilimi rikon sakainar kashi. Yace idana aka cire abun da gwamnatin tarayya ta yi babu jami'a kuma.
Ga karin bayani.