Yajin aikin rukunin likitoci masu neman kwarewa a fannoni daban-daban wadanda ke aiki a asibitocin gwamnatin tarayyar najeriya na ci gaba da gurgunta harkokin kiwon lafiya a kasar, a dai-dai lokacin da manyan likitoci da basa cikin yajin aikin ke kokawa kan mummunan tasirin matakan da kananan likitocin suka dauka.
Wakilin sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko da rahoton cewa, yanzu haka dai likitocin sun kwashe watani biyu suna yajin aiki bisa neman wasu abubuwa masu nasaba da bukatu su.
Matakin dai ya gurgunta aiyukan kiwon lafiya a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiyar jama'a mallakar gwamnatin taraiya. A kano kusan al'amurra sun tsaya a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da asibitin kashi dake Dala.
Alhaji Aminu Inuwa, direktan huldar da jama'a na asibitin Mallam Aminu Kano, yace idan aka ce wani bangare na asibiti suna yajin aiki, ba za'a samu yadda ake so ba tunda yanzu ba'a karbar marasa lafiya a kwantar da su.
Sai dai kawai mutum yazo manyan Likitoci su gan shi ya tafi. A saboda haka wadanda suke kwanche, wadanda suka samu sauki an salame su, wasu kuma ance su tafi wadansu asibitocin. Kusan ba kowa a kwance.
A lokacinda wakilin sashen Hausa ya ziyarci asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, ya iske manyan likitoci da wadanda ake kira consultants ne kawai suke bakin aikin. Su kuma yawansu bai kai ya kawo ba.
Dr Andrew Oluko daya daga cikin manyan Likitocin. Yace al'amarin sai dai a hankali. Yace yanayin aikinsu yafi dadi ace kowa da kowa yana nan babu wanda aka rasa. Yayi fatar Allah ya kawo saukin al'amrin domin mutane a gaskiya suna cikin wahala.