Babban sakataren ma’aikatan filayen jiragen sama na Najeriya, Mr Prince Olayinka, ya bayyana cewa suna gudanar da zanga zangar lumana ne bias umurnin kungiyar kwadago ta Najeriya, domin bukin ranar kula da hakkin ma’aikata na duniya, kuma sun zabi yin gangamin ne a babban filin jiragen sama na Murtala Muhammed, dake jihar Legas.
Daya daga cikin dalilan yin wannan tattaki shine ganin yadda kamfanoni da dama dake aiki a karkashin ma’aikatar kula da filayen jiragen Sama wadanda basa bin ka’idoji wajan kula da hakkin ma’aikata, dan haka wannan tunatarwa ce gare su, kan bukatar bin ka’idoji na duniya kamar yadda suke a tsarin kungiyar kwadago ta duniya wato ILO.
Da yake amsa tambayar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Babangida Jibrin ya yi masa, Mr Prince, ya bayyana cewa tattakin bazai hana matafiya ci gaba da harkokin tafiye tafiyen su ba, domin hatta su kansu fasinjoji zasu so suga an inganta harkokin tafiye tafiye a kasar.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da wannan gangami, suma ‘yan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwanci a harabar filayen jiragen sama kokawa suka yi a kan musguna masu da suka ce anyi kamar yadda daya daga cikin su ya bayyana cewa an hana su gudanar da harkokin su a filin tashin jiragen saman.
wakilinmu na legas Babangida Jibrin ya halarsci gangamin ga kuma rahoton sa.
Your browser doesn’t support HTML5