Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Najeriya Ana Ci Gaba da Tabka Muhawara kan Sake Fasalinta


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

'Yan Najeriya na ci gaba da yin muhawara akan sake fasalin kasar da kuma irin abun da suke so a bar ma bangarorin kasar su gudanar to amma fa kamar yadda Onarebul Namdas ya fada komi ya ta'allaka ne ga 'yan majalisa domin su ne suke doka

Yanzu haka dai a Najeriya ana ci gaba da tabka muhawara a kan batun sake fasalin makomar kasar ta fuskar mulki da zamantakewa.

Tuni ma har wasu jihohi sun amince da su goyi bayan batun sake fasalin kasar, musamman ta fuskar tsarin raba iko tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin.

Jihohin dai na ganin kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta bar musu bangarorin lafiya da sufuri da aikin kashe gobara da sauran wasu fannoni, yayin da ita kuma zata mayar da hankali kan harakokin tsaro da na kasashen waje da kuma kudi.

To sai dai kuma yayin ake cigaba da cece-kuce game da wannan batu na sake fasalin kasar, an fahimci cewa a bisa doka ‘yan Majalisar Dokokin kasar ne kawai ke da hurumin duba batun.

To ko wadanne matakai zasu dauka akan lamarin?

Hon.Abdurrazaq Namdas dake zama shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Wakilan Najeriya yace tuni suka kafa kwamitin da zai ji ra’ayoyin jama’a akan dacewa ko rashin dacewar sauya fasalin kasar.

Shima tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) ya bayyana cewa tsarin da aka gina Najeriya a kansa yanzu yana da matsaloli masu tarin yawa.

Ga rahoton Ibrahim Abdul’Aziz akan wannan batun.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG