Kamar yadda rahotanni ke cewa dan sadan ne ya soma bude wuta ga wasu direbobi dake kan hanyar zuwa cin kasuwa bayan ya nemi su bashi cin hanci, koda suka bashi Naira hamsin sai ya ki karba.
A kan haka ne ganin suna kokarin kama hanyar tafiya sai kawai ya budewa direbobin wuta, lamarin da ya har zuka fasinjoji suka yi masa a ture.
Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ma kakakin rundunar SP Othman Abubakar, ya ce suna bincike.
Yanzu haka dai akwai alamun sauran rina a kaba game da umarnin cire shingayen binciken 'yan sanda da kuma karbar cin hanci da sufeta janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya bada a makon jiya.
Wannan umarni dai da farko yasa 'yan Najeriya, da yawa yin maraba da wannan mataki domin galibi shingayen tamkar hanyar damar karbar na goro ce daga matafiya da kuma masu jigilar kayayyaki.
Domin karin bayani saurari rahoton Ibrahim Abdul'aziz a nan.
Facebook Forum