Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taron Inganta Wutar Lantarki A Jihar Filato


Masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki sun bayyana irin dinbin matsalolin da ‘yan Najeriya, ke fuskanta a sanadiyyar rashin wutar lantarki.

A wani taron yini guda, kamfanin rarraba wutar lantarki a jihohin Benue da Nasarawa da Bauchi da jihar Plateau, ya gudanar a Jos, kamfanin ya bayyana cewa ya shirya taronne domin sauraren irin matsalolin da masu amfani da wutar lantarki ke fuskanta da zummar inganta hidimar su ga al’umma.​

Mahalarta taron wadanda suka hada da sarakunan gargajiya da shugabanin al’umma da masana’antu da masu amfani da wutar lantarki a gidajen su, sun bayyana cewa tsauwala kudin wuta ba tare da samun isassar wutar ba, da rashin karfin wutar na daga cikin abubuwan da ke ci masu tuwo a kwarya.

Daya daga cikin mahalarta taron ya bayyana cewa kudin wutar da suke biya a jihar Filato ya fi na jihar Legas tsada, kuma koda magidanci ya kashe wutar gidansa da rana domin gudun shan wutar da yawa, mitar bata daina kirgawa.

Shima Injiniya Jack Dung, ya bayyana cewa al’ummar yankin su, sun tara kudi kusan sama da Naira Miliyan biyu, domin sayen tukunyar wutar lantarki, da wayoyi da dogayen sanduna amma har yanzu basu sami intantacciyar wutar lantarki a yankin nasu ba.

Daga shiyyar kudancin jihar Filato, wanda suma suna daga cikin masu fuskantar matsalar wutar lantarki, galadiman wase, Alhaji Ummar Mustapha, ya ce babbar matsalarsu ita ce, sau guda suke samun wutar cikin wata guda, kuma rayuwar akasasrin matasan yankin ta ta’allaka ne a kan wutar lantarki.

Zainab Babaji Na Da Cikakken Bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG