Daya daga cikin shugabannin ma’aikatan asibitin kwararru ya bayyana halin da suke cikin na ban tausayi, inda yace suna aiki ne karkashin jiha wanda aka daukesu aiki na tsawon shekaru biyu da watanni uku, an kuma rarrabasu asibitocin dake jiha da ma na kananan hukumomi domin gudanar da aiki.
Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz, yayi kokarin ji daga bakin shugabannin asibitin amma basu ce komai ba duk kuwa da cewar basu bane da alhakin ‘dauka ko biyan ma’aikatan ba. Don haka ne Ibrahim ya zarce zuwa ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Adamawa, inda nan ma bai sami sa a ba.
A baya dai kwamishinan yada labaran jihar Adamawan kwamarad Ahmad Sajo, wanda ya danganta tsaikon da aka samu da almundahana da aka samu wajen daukar ma’aikatan, lamarin da yasa har aka kafa kwamitin bincike.
Fatan wadannan ma’aikata dai shine a samu a biya su albashinsu ko sa rage radadin bashin da suke fama da shi.
Saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5