Babu shakka bude kan iyakoki nada nashi illolin da matsaloli kamar yadda masana tattalin arziki ke cewa amma da ya kamata a san cewa ba rufe kan iyaka zai farfado da tattalin arziki ba nan take, inji Masari.
Masari yace a bari tukunna a farfado da masana'antu a kuma noma abinci duk da cewa manyan masana na cewa sai an rufe kan iyaka za'a shawo kan tabarbarewar tattalin arziki. Wasu ma cewa suka yi rufe kan iyakoki zai sa 'yan Najeriya su zabura su tashi su farfado da masana'antu da aikin noma.
Ibrahim Masari yace babu kayan aikin noma na zamani kuma babu abun dake aiki saboda haka lokacin da shugaba Buhari ya amshi mulki komi ya durkushe. Yace babu abun da ba'a yiwa targade ba a kasar. Duk wata hanyar samar da kudin shiga an watsar komi ya ta'allaka ga man fetur.
Ga firar da abokin aiki yayi da Ibrahim Masari da karin bayani.