Kungiyar da ta fantsama tana zanga zanga tana yin hakan ne domin nuna rashin jin dadinta da rushe wuraren kasuwanci na masu karamin karfi da nakasassu da gwamnatin Legas tayi tare da hana bara da sunan tsaftace birnin Legas.
Tun ba yau ba ne gwamnatn jihar Legas ta fara daukan wannan mataki a wani abu da tace na kawar da bata gari ne baicin tsaftace birnin.
A cewar masu zanga zangar matakin da gwamnatin jihar ke dauka mataki ne na gallazawa masu karamin karfi wadanda ke neman na sawa a baka duk da matsalar tattalin arziki da kasar ke fama dashi. Akasarin masu zanga zangar sun bayyana bacin ransu ne dangane da kokarin da su keyi na ganin cewa sun sami sana'o'in kansu ba tare da tallafin gwamnati ba, amma a maimakon su samu tallafin sai gwamnatoci suka juya masu baya. Bugu da kari sai gashi gwamnati na rusa masu wuraren sana'o'in nasu.
Malam Muhammad Nasiru Dan Adam shugaban matasan makafin birnin Legas ya bayyanawa Muryar Amurka dalilinsu na shiga zanga zangar. Yace gangamin na nunawa gwamnati kukansu ne bisa cin zarafi da wulakanci da kaskanci da tozarci da akeyi masu. Ya fada haka ne saboda wurin da ake ajiyesu za'a samu mutane sittin ko arba'in a daki daya kuma a nan suke kashi da futsari. Idan kuma zasu yi salla nan wurin su keyi. Abincin da ake basu wai ko dabbobi ba zasu ci ba.
Masu zanga zangar sun mika kukansu ga gwamnatin jihar Legas.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.