Bayanai dai sun nuna cewa mutumin da ya mutu dama wadanda suka ji raunin, daman can marasa lafiya ne dake kwance suna jinya a wannan Asibiti wanda shima tuni ya kone kurmus. Baya ga Asibitin gobarar tayi sanadiyar konewar gidaje 8 tare da motoci 3 da kuma shaguna da dama.
A halin da ake ciki dai hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, tace tana tattara yawan adadin asarar da akayi kuma suna kokarin samar da matsugunnai ga wadanda gidajensu suka kone. A cewar Mallam Garba Salihu, jami’in hukumar a jihar Neja yace idan aka kiyasta anyi asarar sama da Naira Miliyan Goma a gobarar.
Har ya zuwa yammacin jiya Litinin wuta na ci gaba da tashi a jikin tankin. Rundunar ‘yan sandan jihar Neja dai ta tabbatar da afkuwar wannan lamari, inda kakakin ‘yan sandan DSP Bala El-Kana yace direban tankarma ya samu rauni amma yana hannunsu.
A Najeriya dai ansha tafka asarar rayukan jama’a, dama dinbin dukiya a sakamakon gobarar Tankar dakon Man Fetur.
Saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.