Da wani zaman dirshen din da suka gudanar a cibiyar Orange Nigar ne ma’aikatan kamfanin kasar Faransa suka fara wannan yajin aiki na kwanaki biyu, wanda a cewarsu mataki ne da ya biyo bayan lura da yadda shugaban kamfanin mai barin gado ke shirin fita daga Nijar, ba tare da an tantance yadda makomarsu za ta kasance ba a hannun wadanda suka karbi jarin kamfanin.
Ma'aikantan kanfanin ta wani bangare suka ce ba za su yadda da dukkan wani yunkurin rage yawan ma’aikatan da sabbin shuwagabanin kamfanin na Orange suka sa gaba.
Biliyan 52 na CFA ne ake tsammani cewa ya shiga aljihun Orange Nigar a matsayin ribar shekarar 2018, inji wasu ma’aikata. Saboda haka su ke ganin ya zama dole a basu kashin da doka ta yi tanadi dominsu.
‘Yan jarida na cikin gida da waje sun kwankwasa kofar babban Daraktan kamfanin na Orange Nigar don jin matsayinsa akan kukan ma’aikatan, amma an ce babu damar ya yi magana a halin yanzu.
Wannan shine karon farko da ma’aikatan Orange Nigar ke jingine aiki, tun bayan kafa kamfanin a shekarar 2008, al'amarin da halin yanzu ya fara shafar harkokin masu amfani da layin Orange Nijar, inji Alhaji Salissou Amadou na Kungiyar Sauvons Le Nijar.
Wasu ‘yan Afirka ta tsakiya ne suka yi nasarar saye hannayen jarin kamfanin Orange Nijar.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5