Cinikin baki a matsayin bayi, ko jefa ‘yan cirani a kurkuku ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, har ma da karkashe wadanda aka yi katarin karar kwana, na daga cikin matsalolin da ‘yan ciranin Afirka ke fuskanta a Libya, duk kuwa da cewa kasar ta rattaba hannu akan dukkan yarjeniyoyin mutunta hakkin dan adam.
Dalili da kenan kungiyoyi masu zaman kansu irin su AEC suka shirya wannan mahawara, domin neman mafita.
Rashin biyan ma’aikata ‘yan cirani hakkinsu wani abu ne da ya zama ruwan dare, kamar yadda wata ‘yar Najeriya ta bayyana wa wakilin Muryar Amurka. Inda ta ce ta je Libya neman kudi a shekarar 2014 amma sai da ta shafe watanni, sannan ubangidanta ya ce ba zai biya ta ba, saboda yana ganin ita ba 'yar kasar ba ce.
Halin da ake ciki a kasar Libya wani abu ne da alamu ke nunin ya sha gaban jami’an diflomasiyar da kansu, inji wani dan Nijar Maman sani.
Daraktan ma’aikatar hulda da jama’a a ofishin jakadancin Libya a Nijar Vissam Omran wanda ya halraci wannan mahawara, ya jaddada niyar isar da sako zuwa gaba, kuma a cewarsa hukumomin kasarsa za su yi wani abu akai, domin magance wannan matsala ta cin zarafin ‘yan Afrika.
Hukumar kare hakkin dan adam ta kasar Nijar wato CNDH dake jagorancin wannan yunkuri na jami’an fafutika, ta sha alwashin tuntubar kungiyoyin kasa da kasa irinsu ECOWAS, da UEMOA da kuma AU domin duba hanyoyin da za a bullowa wannan al'amari.
Kungiyar EU na daga cikin wadanda ake zargi da hannu a abubuwan dake faruwa da ‘yan Afirka a Libya, saboda haka aka gayyato wakilanta a wurin wannan mahawara.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muaryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum