A jiya Laraba ne wasu ma’aikatan hukumar binciken sararrin samaniya ta Amurka NASA, suka yi tattaki a duniyar wata, don gyara wani famfon iska na wata na’urar bincike da aka dasa a duniyar wata.
Fitowar farko Mr. Drew Feustel, sai Mr. Ricky Arnold, sun garzaya domin duba matsalar dake damun na'urar sanyayya famfon, hukumar na kokarin ganin ta samar da na’urori masu nagarta a kowane lokaci.
Daya daga cikin famfon na’urar ya samu tangarda a dalilin daukewar wuta da aka samu na tsawon kimanin shekaru goma sha bakwai da ake kira “Frosty” ma’aikatan lafiya na hukumar sun ja hankalin ma’aikatan binciken dake sararin samaniya, da suyi hattara game da kubucewar gurbatacciyar iska da zata iya yi masu lahani.
Yanzu haka dai ma’aikatan hukumar bincike su shida dake cikin duniyar wata zasu kammala gyaran, inda ake shirin aika wani jirgi kirar ‘Orbital ATK’ a ranar lahadi mai zuwa.