Ma’aikata a Najeriya sun amsa kiran gamaiyar kungiyar kwadago wajen shiga yajin aikin neman karin mafi karancin albashi zuwa Naira 494,000 da rage tsadar lantarki.
A babban birnin Abuja ma'aikatu, da bankuna, da ma sauran sassa da su ka shafi gwamnati sun kasance a rufe.
Wunin farko na yajin aikin ya nuna yanda zafin yajin ya ke don yadda ya dakatar da aiyukan gwamnati cak inda hatta kan tituna da aka saba ganin cunkoson motoci a irin ranar Litinin kan zama shara-shara ko ma wayam don ma'aikata sun yi zaman su a gida.
Jami'an kungiyar kwadagon sun shiga zagawa ma'aikatu don tabbatar da duk ma'aikata sun bi wannan umurnin.
Mukaddashin sakataren kungiyar kwadago ta TUC Kwamred Hassan Salihu Anka ya ce tamkar gwamnati ta yi biris ne da bukatun ma'aikata.
Da ya ke amsa tambayar da Muryar Amurka ta masa kan shin ba yajin zai iya zama a fara kamar da gaske sai can a janye ba,? Komred Anka ya amsa cewa, "Allah dai ke da gobe, ba wanda ya san gobe, amma dai wanan yajin aiki, yajin aiki ne na kasa baki daya, kowa ya na ciki, ko mai sayar da Pure Water ma ya na cikin wannan yajin aikin don ya na ji a jikinsa. Maganar ma a dage yajin aiki, duk bai taso ba."
Yajin aikin dai ya shafi hatta filayen jiragen sama da su ka zama sai kwarya-kwaryan aiki.
Za a zuba ido a ga yanda gwamnati za ta iya shawo kan ma'aikatan daga yanda ta cije kan biyan Naira 60,000.
Ma'aikatan lantarki ma sun dau matakin kashe wutar inda birane su ka dau rugugin na'urorin samar da wuta musamman a gidajen 'yan jari hujja inda su kuma talakawa dama tamkar alfarma ce ganin hasken wuta a gidajensu.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5