A daidai lokacin da hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya ta tsunduma yajin aikin gama gari, Ministan Kudin Kasar, Wale Edun yace bukatun ma'aikatan nada matukar tsada.
"Don haka, ba kawai kana tsayar da albashi ga iya ma'aikatan gwamnatin tarayya ba ne, misali kana tsayar da mafi karancin albashi ne daya zama wajibi ga jihohi da kananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu dama kananan 'yan kasuwa su biya."
"Wani abune dawamamme, ba wai ma'auni ba. don haka, akwai abin lura akan yadda ake yanke mafi karancin albashi a baya, musammanma abinda muke kira da sakamakon sauyi, wanda idan akayi la'akari da abinda 'yan kwadago ke bukata a yanzu, zai kasance mai matukar tsada ga dukkanin matakan.
Kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC sun ce mafi karancin albashin da ake amfani da shi a halin yanzu na Naira dubu 30 ba zai iya biyan bukatun matsakaicin ma'aikaci a Najeriya ba, inda suka koka da cewar har yanzu gwamnonin jihohi na amfani da shi duk da wa'adinsa ya kare a watan Afrilun daya gabata, shekaru 5 bayan da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu akan dokar mafi karancin albashi ta 2019.
Kamata yayi a rika sake nazarin dokar duk bayan shekaru 5 domin dacewa da bukatun tattalin arzikin ma'aikata.
Dandalin Mu Tattauna