Jam’iyyar Labour ta shaidawa hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya cewar tayin Naira dubu 494 a matsayin mafi karancin albashi “ba abune mai yiyuwa ba.”
Bisa kafa hujja da hauhawar farashin kayan masarufi da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki a Najeriya, kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun bada tayin Naira dubu 615, 500 da Naira dubu 494 a matsayin sabon mafi karancin albashin Najeriya, kowacensu.
A yau Litinin kungiyoyin kwadagon suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon kin amsa bukatunsu da gwamnatin tarayya tayi.
A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), Kakakin Jam’iyyar Labaour, Obiora Ifoh, ya bukaci kungiyar nlc ta jingine yajin aikin tare da komawa kan teburin tattaunawa da gwamnatin tarayya.
A cewar obiora, yajin aikin na iya kara tabarbara halin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Najeriya.
Obiorah yace, “martanin na farko shine kada hadaddiyar kungiyar kwadago ta jefa ‘yan Najeriya cikin karin wahalhalu”.
“Tuni ‘yan najeriya ke fama da dimbin matsaloli kuma bama bukatar a sake ta’azzara lamarin”.
“Bana tunanin tayin Naira dubu 494 a matsayin mafi karancin albashi abune mai yiyuwa. gaskiya ba zai yiyu ba”.
“Wannan adadi ne da ba zai dore ba saboda hakan na nufin najeriya zata yi amfani da dukkanin kudadenta wajen biyan albashin ma’aikata”.
“A cigaba da tattaunawa har sai an samu mafificiyar matsaya.”
“Bukatar ma’aikatan najeriya su zauna a gida zai shafi komai, ciki harda tsadar rayuwa kuma ‘yan najeriya ba zasu iya jure hakan ba. tattaunawa ba abune na lokaci guda ba”.
“Idan gwamnatin tarayya bata son mafi karancin albashin ya haura naira dubu 60, ina ganin kamata yayi hadaddiyar kungiyar kwadago tayi amfani da abunda ya samu a yayin da take cigaba da tattaunawa”.
Dandalin Mu Tattauna