Luiz Suarez Ya Dawo Buga wa Kasarsa Ta Uruguay Kwallo

Luiz Suarez

Dan shekara 36, Suarez na daya daga cikin ‘yan wasa masu yawan kwallaye a gasar Brazil inda yake da kwallaye 14 a wasanni 29.

Luiz Suarez ya dawo taka wa kasarsa ta Uruguay leda inda kasar za ta kara a wasannin shiga gasar cin kofin duniya guda biyu.

Daya daga cikin wasannin da Argentina ne.

Dan shekara 36, Suarez na daya daga cikin ‘yan wasa masu yawan kwallaye a gasar Brazil inda yake da kwallaye 14 a wasanni 29.

A ranar Alhamis Uruguay za ta kara a Buenos Aires sannan kwana biyar bayan wasan ta fafata da Bolivia.

Argentina wacce ke rike da kofin gasar ta kasance a gaba a teburin wasannin da maki 12.

Uruguay, Brazil da Venezuela n biye da ita da maki bakwai-bakwai a wasanni hudu.