ABUJA, NIGERIA -Kungiyar likitoci da ke fadakarwa kan abubuwan da ke kawo cutar daji da kuma hanyoyi kariya ta Najeriya, ta gudanar da taron karawa juna sani kan sabbin hanyoyin maganin cutur daji. Taken taron na wannan shekarar shine ‘Sabunta yadda ake maganin cutar daji a Najeriya.
A duk shekara likitoci a bangaren maganin cutar daji kan hallara don tattaunawa da fadakarwa kan sabbin hanyoyin maganin cutar daji da kuma binciken da ake yi na kimiya game da cutar.
Kwararriyar likita a bangaren maganin daji ta fannin gashi wadda ake kira Chemotherapy a turance Dr. Hannatu Ayuba Usman ta ce irin wannan taron kan zai taimaka wajen wayar da kan jama’a game da cutar daji da maganin ta, da kuma sanin irin hanyoyin da ya kamata abi don samun waraka daga cutar.
Haka kuma taron ya duba yadda za a ba wa masu fama da cutar daji cikakken kulawa ta yadda za suyi rayuwa mai inganci a cikin al’umma kamar a cewar Dr. Shehu Salihu Umar.
Dr. Mustapha Muhammad ya ja hankalin mutanen ne da nuna muhimmancin zuwa asibiti a lokacin da cutar ta soma, hakan zai taimaka wajen shawo kan cutar da kuma magance ta.
Shima Dr. Abba Aliyu Tijjani ya ce sun koyi sabbin hanyoyin kimiya ta yadda zasu rika duba marasa lafiya.
A nasa bangaren kwararre a fanni harhada magunguna Dr. Richard Mishelian ya ce da taimakon gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu yanzu ana samun magungunan cutar daji da rahusa, suna kuma fata nan gaba a rika samun magungunan kyauta.
An ware watan gobe ne a matsayin watan wayar da kan jama’a game da cutar daji.
Saurari cikakken rahoto daga Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5