Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 Na Barazana Ga Zabiya


Albino - Zabiya
Albino - Zabiya

A Najeriya nau'in mutanen da ake kira zabiya ko Albino a turance sun ce cutar covid 19 ta haifar musu da babbar illa wadda har ke barazana ga salwantar rayukan su.

Duk da yake babu bayyanannun alkaluma na adadin mutanen da ake kira zabaya da suka kamu da cutar covid 19 a Najeriya, amma illar da cutar tayi ga kasashen duniya suma ta haifar musu da matsala.

A wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya inda ake da matsanancin zafin rana, baya ga wannan matsalar ta karancin taimako da suke fuskanta, basu da karfin jiki da kan iya jurewa yanayin ko gudanar wani aikin karfi na samun dogaro da kai.

Albino - Zabiya
Albino - Zabiya

Sai dai a jihar Kebbi matar gwamnan Dr. Zainab Bagudu wadda ta ciri tuta wajen yaki da cutar ciwon daji ko cancer ta yanke shawarar tallafa musu da tallafin covid 19 domin rage radadin halin da suka samu kansu ciki.

Ga irin wadannan mutanen tallafi baya da kadan duba da irin wahalhalun da suke fuskan ta, akan haka ne ma ta kara da yin kira ga jama'a akan.

“A nuna kulawa da bayar da taimako ga zabaya kuma a dauke su tamkar sauran jama'a ba tare da nuna musu bambanci ko kyama ba"

Kulawa da wannan nau'in na jama'a kan iya ceto rayukan adadin su da aka kiyasta ya haura miliyan 2 a Najeriya.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

XS
SM
MD
LG