Rahotanni daga Kanon Najeriya na cewa ana ci gaba da samun karin mace-mace a jihar wadanda babu takamaiman bayanan da suke nuna me ke haddasa su.
Mace-mace na faruwa ne yayin da ake kokarin dakile yaduwar kwayar COVID-19 da ke haddasa cutar Coronavirus – annobar da ta addabi sassan duniya.
Rahotanni da dama sun ruwaito yadda mace-mace suka fara aukuwa a makon da ya gabata a birnin wanda ke da miliyoyin mutane.
Amintattun kafafen yada labarai, sun ruwaito masu ayyuka a makabartun jihar suna cewa, sun ga karin adadin mutanen da ke mutuwa a kullum.
Wasu majiyoyi sun ce kiyasin mace-macen a makabartun ya kai daruruwa.
Sai dai jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hukumomin jihar sun bayyana cewa an sanar da su mace-macen da ke faruwa, amma sun ce ba su da alaka da cutar coronavirus.
Ya zuwa ranar Juma’ar da ta gabata, Hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC ta ce mutum 77 ne suka kamu da cutar ta COVID-19 a jihar yayin da mutum guda ya mutu.
Tuni dai gwamnatin jihar ta ce ta kaddamar da wani bincike na musamman domin gano musabbanin wadannan mace-mace, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a yau Litinin.
Wannan al’amari ya janyo ka-ce-na-ce sassan Najeriya inda masana a fannin kiwon lafiya suka fara tsokaci kan abin da ke faruwa.
Dr. Grema Bukar, likita ne asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH,) ya kuma ce babu wata hujja da za ta nuna cewa cutar coronavirus ce ta ke haddasa mace-mace ko akasin hakan.
“Ba za ka iya cewa kai-tsaye yana da alaka coronavirus ba, saboda ba gwada wadanda suka rasu aka yi ba saboda suna gida, wadansu ko da a asibiti aka yi ba a dauka an gwada an tabbatar ba.” In ji Bukar.
“An rage ayyukan da ake yi na yau da gobe a asibitoci domin a mayar da himma kan masu zuwa neman kulawar gaggawa don COVID-19.”
Sai dai ya ce, ta yi wu, yanayin da aka shiga a yanzu ka iya haifar da wannan al’amari.
“Yanayin da muka shiga a yanzu, yawancin asibitocin da suke aiki, an rage ayyukan da ake yi na yau da kullum.”
Hakan a cewar likitan zai iya shafar yadda ake kulawa da masu fama da wasu cututtuka kamar na hawan jini, ciwon sukari, cutar daji da dai sauransu.
“Idan kana fama da wata cuta kuma ka ji an ce ba za a karbe ka a asibiti ba, sai kana da bukatar kullawar gaggawa, hakan na janyo mutane su yi zamansu a gida.”
Daga karshe Dr. Grema Bukar ya ce a matsayinsu na masu kulla da fannin kiwon lafiya, hukumomi har yanzu ba su fito suka bayyana musu komai dangane da wadannan mace-macen ba.
A shafukan sada zumunta ma yayin da wasu matasa da dama suka dukufa yi wa Kano adu’o’i kan halin da ta tsince kanta, wasu kuwa na ta nuna baccin ransu kan yadda gwamnatin jihar ta ki cewa komai game da lamarin.
Facebook Forum