Likitoci Sun Ayyana Yajin Aikin Kwanaki 3 A Abuja

ADAMAWA: Likitoci a FMC Yola sun raba tagwayen da aka haifa a manne da juna

Yajin aikin na zuwa ne bayan cikar wa’adin makonni 3 da likitocin suka bayar a shekarar da ta gabata.

Reshen birnin tarayyar Najeriya, Abuja, na kungiyar likitoci masu neman kwarewa (ARD, FCT) ya tsunduma cikin wani yajin aikin gargadi na kwanaki 3 a kan bashin kudaden albashi da alawus-alawus dama sauran bukatu.

Yajin aikin ya dakatar da ayuuka a asibitocin gwamnatin dake birnin abuja.

Shugaban kungiyar likitocin na ARD FCTA , Dr. George Ebong, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Laraba.

A cewar Dr. Ebong, yajin aikin na zuwa ne bayan cikar wa’adin makonni 3 da likitocin suka bayan a shekarar da ta gabata.

Da yake magana a madadin kungiyar ARD, Dr. Ebong ya koka game da rashin kulawar da ake nunawa asibitoci da likitoci a babban birnin tarayyar Najeriya.

Ya yi kira ga ministan babban birnin, Nyesom Wike, da ya shiga tsakani domin kaucewa matakin rufe asibitocin har sai illa masha Allah.

A cewarsa, shawarar shiga yajin aikin gargadin na kwanaki 3 ta samo asali ne daga babban taron mambobin kungiyar daya gudana a jiya Talata.