Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Fuskantar Matsalar Karancin Masu Ba Da Tallafin Jini


Wata mata tana ba da tallafin jini a asibiti
Wata mata tana ba da tallafin jini a asibiti

Hukumar Kula da Jini ta kasa ta Najeriya ta ce a shekarar 2023 kasar tana samun kusan kashi 27 cikin 100 na jinin da ake bukata, abin da masana suka ce ya gaza matuka.

Najeriya ta fara wani shiri na bayar da jini yayin da kasar ke fuskantar karancin jini.

Hukumomi sun ce Najeriya na samun kashi daya bisa hudu kawai ne na jinin da ake bukata a kowace shekara, wanda hakan ke barin majinyata da asibitoci cikin tsananin bukatar jini a gaggawa.

Mawakin Najeriya, Excel Praiseworth, ya shafe shekaru 30 yana fama da cutar sikila.

A watan Yuli, rashin lafiyar da ke da alaka da cutar ya kawo masa matsanancin ciwo, har sai da aka yi masa karin jini.

“Ba a samu jini a asibiti ba. Ina tsammanin bankin jininsu ya kare. Ban ma sani ba ko suna da bankin jini tun farko. Don haka dole muka fara neman jini.” In ji Praiseworth.

Praiseworth ya jira fiye da awa biyar kafin wani danginsa ya bayar da jini, kuma a karshe ya samu sauki.

Hukumar Kula da Jini ta kasa ta Najeriya ta ce a shekarar 2023 kasar tana samun kusan kashi 27 cikin dari na kimanin yanki miliyan 1.8 na jinin da ake bukata a kowace shekara daga masu ba da jini na sa kai.

Hukumomin lafiya na Najeriya suna danganta rashin son ba da jini da rashin ingantattun bayanai, son zuciya na al'adu da addinai, da karancin kudaden gudanar da ayyukan Hukumar Kula da Jini ta kasa, wanda ya hada da wayar da kan jama'a.

Matsanancin karancin jinin da Najeriya ke fama da shi sau da yawa yana tilasta wa marasa lafiya neman taimako daga wadanda ake kira ‘yan kasuwa masu ba da jini — wadanda ke ba da jini ba bisa ka’ida ba.

Domin taimaka wa wajen magance karancin jinin, gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shiri a watan Satumba na kafa Cibiyoyin Tara Jini a dukkanin kananan hukumomi 774 na ƙasar.

Manufar ita ce tabbatar da cewa akwai isasshen jini idan ana bukata da gaggawa.

((Ijeoma Leo-Nnadi, Hukumar Kula da Jini ta Ƙasa)) ((mace, Turanci))

“Akwai wannan rashin sha’awar ba da tallafin jini. Mutane ba sa son bayar da jini. Suna tunanin idan sun ba da jini za su iya mutuwa saboda ba su da isasshen jini. Muna kuma zuwa manyan makarantu inda muke da matasa da yawa, kuma muna zuwa coci-coci da suke cike da jama'a. Muna zuwa kasuwanni. Muna zuwa shagunan sayayya.” In ji Ijeoma Leo-Nnadi, jami’a a hukumar Kula da Jini ta kasa.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ware 14 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar ba da tallafin jinni ta duniya.

Fassarar Rahoton: Timothy Obiezu daga Abuja.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG