Libya Ta Kama ‘Yan Najeriya 2 Bisa Zarginsu Da Fataucin Miyagun Kwayoyi 

Miyagun Kwayoyi

Sanarwar da wata kungiya mai rajin ceton bakin haure “Migrant Rescue Watch”, ta wallafa a shafinta na X, tace an kama mutanen ne a garuruwan Sabha da Bani Walid.

Hukumomin Libya sun ce sun kama wasu ‘yan Najeriya 4 bisa zarginsu da fataucin miyagun kwayoyi da kuma kamuwa da cututtuka masu yaduwa.

Sanarwar da wata kungiya mai rajin ceton bakin haure “Migrant Rescue Watch”, ta wallafa a shafinta na X, tace an kama mutanen ne a garuruwan Sabha da Bani Walid.

Garin Bani Walid, dake kudancin birnin Tripoli, ya shahara a matsayin tashar da bakin hauren dake nufin ketarawa zuwa Turai ke taruwa.

A Sabha, hukumar binciken manyan laifuffukan Libya ta gudanar da samame a gidajen wasu ‘yan Najeriya 2 da ake zargi tare da kwace kwayoyin dake sanya maye guda 1, 200 da sauran haramtattun kaya.

An mika mutanen 2 ga jami’an tsaron garin Sahba domin zurfafa bincike.

A wani al’amarin na daban kuma, an tsare wasu ‘yan Najeriya 2, mace da namiji a garin Bani Wani bayan da gwajin lafiyar da aka gudanar akansu ya nuna cewar suna dauke da cututtukan da ake iya yadawa.