Hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC) ta soke cancantar shiga zabe ga ‘yan takara daban-daban a zaben kananan hukumomi da za ta yi a karshen wannan wata na Oktoba.
KANSIEC ta dauki wannan mataki ne bayan samun su da matsalar tu’ammali da ababen sanya maye yayin wani gwaji da aka yi.
“Za mu rubuta takarda zuwa ga jam’iyyunsu cewa mun samu matsaloli tare da ‘yan takararsu da kuma kwafin takardar sakamakon takardar NDLEA.
“Kowane NDLEA na fada mana cewa wannan ganye yake sha, wannan taramol har da cocaine ma (hodar iblis).” In ji Kwamishinan hulda da kafafen yada labarai na hukumar zabe a jihar Kano, Alhaji Lawal Badamasi Gezawa.
“Don haka, mun mayarwa da jam’iyya. Ita kuma jam’iyya za ta canjo dan takarar da za ta tsayar wanda shi ma za a tantance shi.” Gezawa ya kara da cewa.
A cewar Gezawa ba za su bayyana sunaye ko jam’iyyun da ‘yan takarar suka fito ba yana mai cewa hurumi ne na jam’iyyun su bayyanawa jama’a idan suna so.
Sai dai masu rajin shugabanci na gari sun kalubalanci matakin hukumar na boyen sunayen mutanen da ta soke takarar su duba da cewa mukami na jama’a da ‘yan takarara za su rike.
A cewar Darektan Kungiyar Ocean da ke aikace-aikacen wayar da kan ‘yan kasa da horar da ‘yan siyasa kan shugabanci nagari, Comrade AbdulRazaq Alkali kamata ya yi hukumar ta KANSIEC ta sanar da jama’a sunayen ‘yan takara.
“Ya kamata a ce ta bayyanawa jama’a wadanne jam’iyyu ne, kai har sunayen mutanen ma za sui ya bayyanawa saboda mukamai ne na jama’a, saboda mutane suna da hakkin su san wane ne kai, su kuma san dabi’arka.
“Domin yanzu, an bar jama’a a duhu a siyasance ba mu san jam’iyyu gudanawa ne kuma ba mu san wadannan ‘yan takara ba.”
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Dandalin Mu Tattauna