Wata Babbar kotun tarayya a Legas da ke kudancin Najeriya ta yankewa wata ‘yar kasar Canada hukuncin zaman gidan yari tsawon shekaru 11.
Kotun a ranar Laraba ta ayyana cewa ta samu Adrienne Munju da laifin shigar da tabar wiwi mai nauyin kilo 35.20 cikin Najeriya.
Hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi ta NDLEA ce ta kama Munju mai shekaru 41 a Filin tashin jirage na Murtala Muhamamad da ke Ikeja a birnin Legas a ranar 3 ga watan Oktoba.
Sai dai kotun ta ba Munju zabin biyan Naira miliyan 100 kan tuhume-tuhume guda biyu da aka same ta da laifi akai.
Mai Shari’a a kotun Dehinde Dipeolu ya ce an ba Munju zabin biyan kudaden en saboda ta amsa cewa ta yi laifi.
Justice Dipeolu convicted and sentenced Muju to the term of imprisonment after she pleaded guilty to the charge preferred against her by NDLEA.
“Mai Shari’a Dipeolu ya same Muju da laifi ya kuma yanke mata hukunci bayan da ta amsa laifi.” In ji wata sanarwar da Darektan yada labarai na NDLEA Femi Babafemi ya wallafa a shafin Facebook.
Dandalin Mu Tattauna