Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Burtaniya Sun Sabunta Yarjejeniyar Yaki Da Miyagun Kwayoyi

Shugabar HIOI, Victoria Pullen, hagu, da Shugaban Hukumar NDLEA, Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, dama

A cewar Pullen batun fataucin miyagun kwayoyi wani babban al’amari ne na duniya baki daya, kuma kamar sauran manyan kalubale irinsu, sai duniya ta dauki manyan matakan yaki da shi.

Ofishin kula da harkokin kasa da kasa na Burtaniya (HOIO), ya bayyana cewar hadin gwiwar da yake yi da Najeriya a yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi yana haifar da da mai ido, kamar yadda aka gani a jerin nasarorin da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ke samu a baya-bayan nan.

Shugabar HIOI, Victoria Pullen ce ta bayyana hakan lokacin da ta jagoranci abokin aikinta, Kristoffer Hawsfield wajen kai ziyarar aiki ga shugaban hukumar NDLEA, Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, da nufin sabunta yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin HIOI da NDLEA a jiya Litinin.

Shugabar HIOI, Victoria Pullen, hagu, da Shugaban Hukumar NDLEA, Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, dama
Shugabar HIOI, Victoria Pullen, hagu, da Shugaban Hukumar NDLEA, Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, dama

A cewar Pullen batun fataucin miyagun kwayoyi wani babban al’amari ne na duniya baki daya, kuma kamar sauran manyan kalubale irinsu, sai duniya ta dauki manyan matakan yaki da shi.

Shugabar HIOI, Victoria Pullen, hagu, da Shugaban Hukumar NDLEA, Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, dama
Shugabar HIOI, Victoria Pullen, hagu, da Shugaban Hukumar NDLEA, Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, dama

A martaninsa, Janar Marwa ya bayyana godiya ga gwamnatin Burtaniya wajen tallafawa kokarin Najeriya na yaki da annobar fataucin miyagun kwayoyi, musamman wajen ginawa tare da bada gudunmowar cibiyar hukumar ta ruwa a makon daya gabata, da kuma samar da irinta a filin saukar jiragen saman Murtala Muhammad dake Ikeja a bara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG