A yau Laraba ne jami’an cibiyar kare hakkoki bil,adama din suka fito da rahoton nasu bayan ziyarar gani-da-ido da suka kai a wasu wurare ukku da ake tsare da sojan Libya tareda jami’an ma’aikatar harakokin cikin gida ke tsare da mutanen a gabashin kasar ta Libya.
Cibiyar ta H-R-W tace a wadanan wuraren dake Benghazi da al-Bayda, akwai mutane kamar 450 da ake tsare da su wadanda kuma akalla rabinsu suka ce an gana musu azaba, yayinda dukkansu suka ce ana hana su ganin lauyoyin da zasu iya kare su, ko ma a kaisu a gaban alkali, kai, ko ma a tuhumce su ba’a yi ba.
Your browser doesn’t support HTML5
Mulkin kasar ta Libya dai yanzu an raba shibiyu a tsakanin gwamnatin dake da amincewar kasashen duniya wacce mazauninta ke a Tobruk da kuma wacce mayakan sa-kai suka kafa, mai hedkwata a Tripoli, babban birnin kasar.