Wata kungiya mai alaka da al-Qaida a Libiya ta fidda jerin wasu sunaye yau Talata na wadanda kungiyar tace sun mutu a hari ta sama da Amurka ta kai, amma bata sa sunan Mokhtar Belmokhtar ba a cikin sunayen, wanda shi ne muhimmin mutum wanda aka auna a harin.
Sanarwar ta Ansar al-Shariah ta musanta cewa akwai kuma wanda suka sutu bayan jerin sunayen.
Hare-haren boma-boman su ne na farko da Amurka ta kai ta sama a Libiya tun rikicin shekarar 2011 da aka yi wanda ya hambarar da dadadden shugaba Moammar Gadhafi. Jami’an Amurka dai basu tabbatar da mutuwar Belmokhtar ba, wanda shine jigo a kungiyar al-Qaida a yankin Mghreb kafin ya kafa tasa kungiyar ta ‘yan ta’adda mai suna Singers In Blood Battalion a shekarar 2012.
Amurka ta zargi Belmokhtar da laifin jagorantar harin da aka kai a wani ginin sarrafa iskar gas a shekarar 2013 a kasar Algeria wanda ya hallaka mutane 37, ciki har da amurkawa 3. Mahukuntan Amurka sun zargi Belmokhtar da laifufuka dake da nasaba da ta’addanci bayan harin bom din.