Gwamnatin Legas na shirin rufe mayankar abatuwa domin a fadada da kuma zamanantar da ita amma masu amfani da mayankan na ganin wannan shiri wani matakin ne hana musu aiwatar da harkokin kasuwancinsu bisa la'akkari da cewa yawancinsu 'yan arewacin Najeriya ne.
"Yanzu mun fara tuntubar baki cewa kar kowa ya lodo saniyarsa, tun da babu inda za ka ajiye kudinka idan ka sayar da ita, an ce za a rushe inda kake ajiyewa kafin a bude banki ka je ka sa." inji Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Legas, Alhaji Abdullahi Laliga
Ya kara da cewa "to dole mu ce kowa ya saurara, idan har ma ka lodo, to ka sauke ko a Ibadan ko a jihar Ogun."
Amma a wata sanarwar da Ma'aikatar harkokin gona ta fitar a jihar, ta musanta zargin cewa ana son ta da su ne daga mayankar domin muzguna musu.
Sai duk da haka ana ganin wannan matakin zai shafi dumbim matasan da ke aiki wannan mayakar.
"A gaskiya yanzu ma muna fama da rashin ayyuka na matasa. Muna da kimanin matasa 7,000 ko 8,000 a abatuwa kuma daga cikinsu bai wuce mutum 3,000 ke da sana'ar yi ba saboda karancin aiki. inji Shugaban matasan, Alhaji Madu Top
Top ya kara da cewa "to wannan matakin zai ja wannan 3,000 su rasa ayyukansu wanda ka iya jefasu wata rayuwa ta zamani,"
Wannan ba shi ne karon farko da jihar Legas ta yi yunkurin rufe wannan mayanka tare da bayyana anniyarta ta inganta ta ba, matakin da 'yan kasuwa ke ganin zai karyasu kuma a shirye suke su koma jihar Ogun.
Your browser doesn’t support HTML5