Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Sama da Mutane 50 a Gwaska a Jihar Kaduna


Jana'iza
Jana'iza

Masarautar Birnin Gwari ta tabbatar da mutuwar sama da mutane hamsin da aka kai musu hari a garin Gwaska a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Adadin mutane da suka mutun a harin da wasu yan bindiga suka kai a garin Gwaska na karamar hukumar Garin na karuwa, kana kuma an samu asarar kadarori da dama biyo bayan kona wani kauye kurmus da maharan suka yi a cikin wannan harin.

Da yake kara tabbatar da adadin mutanen da suka raukarsu a cikin wannan mummunar harin, mai martaba sarkin Gwari Mallam Jibrin Zubairu Mai-Gwari na biyu, yace sun yi jana’izar kimanin mutane 34 kuma sun labara cewa mutane da dama sun mutu a wasu kauyukan karaar hukumar birnin Gwari. Sarkin Gwari ya mika ta’aziyarsa ga iyalan wadanda wannan harin ya rutsa da su.

Wani da ya shedi al’amarin kuma daya daga cikin wadanda suka fara kai dauki bayan harin, yace sun ga gawarwaki da dama a kan hanya da kuma cikin daji. Haka kuma yace sun gawarwaki da aka konasu wasu kuma harbinsu maharan suka yi da bindiga suka kashe su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG