Lebanon Ta Tsagaita Wuta a Yaki Da Kungiyar IS

Rundunar sojin kasar Lebanon ta sanar da tsagaita wuta a yaki da mayakan IS a kan iyakar Syria.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar yau Lahadi tace, an fara aiwatar da tsagaita wutar da karfe hudu da nufin bada damar tattauna da ta shafi makomar sojojin kasar Lebanon tara da aka yi garkuwa dasu a watan Agusta shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, da ake kyautata zaton har yanzu mayakan suna tsare da su.

Mayakan kasar Lebanon Hezbolla, da rudunar sojin Syria dake yakar kungiyar IS a yankin, suma sun sanar da tsagaita wuta.


An yi garkuwa da sojojin kasar Lebanon da ‘yan sanda talatin lokacin da mayakan IS suka kwace ikon garin Arsal dake kan iyakar Lebanon shekaru uku da suka shige. Kungiyar IS ta kashe mutane hudu, na biyar kuma ya mutu sakamakon raunuka da yaji, an kuma saki goma sha shidda a musayar fursunoni da aka yi cikin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.