Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea ta Arewa Ta Yi Gwajin Makamai Masu Linzami


Wasu makamai masu linzami da Korea ta Arewa ta harba a matakin gwaji
Wasu makamai masu linzami da Korea ta Arewa ta harba a matakin gwaji

Korea ta Arewa ta yi gwajin wasu makamai masu linzami guda uku, wadanda bayanai suka nuna cewa ba su kai ga inda aka yi niyyar su kai ba.

Wani kwamandan dakarun ruwan Amurka, ya tabbatar da cewa Korea ta Arewa, ta yi gwajin wasu makamai masu linzami, wadanda suke tafiyar gajeran zango a jiya Juma’a, amma kuma, makaman ba su kai ga inda aka yi niyyar su kai ba.

Kakakin rundunar sojin Amurka a yankin Tekun Pacific, ya ce makamai masu linzami uku Korea ta arewan ta harba, inda ta rika ba da tazarar kusan minti goma-goma a tsakaninsu.

Kakakin ya kara da cewa makami mai linzami na farko da na ukun, sun mutu tun suna sama, sannan na biyun kuma ya tarwatse jim kadan bayan da aka harba shi.

Ya kuma kara da cewa, babu ko daya daga cikin makaman da zai yi barazana ga yankin arewacin Amurka ko kuma Guam, wanda shi ne yanki mallakar Amurka mafi kusa da Korea ta Arewan.

Tun da farko, dakarun Korea ta Kudu, sun sanar da cewa makwabciyarta ta Arewa, ta harba wasu makamai masu linzami da dama daga Lardin Gangwon, wadanda suka ce watakila wani fanni ne na atisayen da sojojin kasar ke yi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG