Lauyoyin dai sun nuna damuwarsu kan rashin samun ganin jagoran kungiyar Shi’a Sheik Ibrahim Zakzaky.
Shugaban kwamitin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa Mai Shara’a Muhammad Lawal Garba, yace lauyoyin basu bayyana ba gaban kwamitin kamar yadda bangaren sojojin Najeriya sukayi, wanda har lauyoyin suka aika da takardar dake nunin cewa har yanzu basu sami damar ganin mutumin da ya dauke su aiki ba, wanda hakan yasa ba zasu gurfana ba.
Hakan yasa kwamitin ya bayar da damar aje ayi binciken inda wanda ya dauki su aiki yake, kwamitin dai yana da damar da zai bayar da ikon a bar lauyoyin su gana da wanda suke karewa, don ci gaba da binciken da akeyi.
Kwamitin yayi alkawarin yin bincike na adalci ga bangarorin biyu da wannan lamari ya faru, yanzu haka ma an baiwa lauya mai kare sojojin aikin ya binciko inda aka tsare shugaban yan Shi’a da kuma hukumar da take tsare da shi.
Your browser doesn’t support HTML5