Wata kungiya da aka fi sani da ‘Kungiyar Lauyoyi ‘Yan Kabilar Igbo' ta tattaro hancin manyan lauyoyinta a fadin duniya, domin shirin ba da kariya ga jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biyafara, a shari’arsa da za’a ci gaba a ranar 26 ga watan nan na Yuli.
Nnamdi Kanu wanda ya arce daga kasar a cikin beli a shekarar 2017, ya kuma shiga hannun jami’an tsaron Najeriya a makon jiya, wadanda suka sake gurfanar da shi a gaban kotu, inda suka sami amincewar tsare shi a hannun jami’an tsaron farin kaya na DSS.
An sami rahotanni mabambanta akan daga inda aka kamo Nnamdi Kanu zuwa Najeriya, a yayin da labari mafi shahara shi ne wanda ke cewa an kamo shi ne a kasar Kenya, duk da yake ofishin jakadancin kasar a Najeriya ya fito ya musanta zargin.
Gwamnatin Najeriya dai ta ci gaba da tsuke bakinta akan cikakken bayanin ainihin yadda ta kamo shi, da kuma daga kasar da ta kamo shi.
Lauyan Kanu, Ifeanyi Ejifor ya yi zargin cewa “an yi masa duka tare da gana masa azaba a Kenya, kafin mika shi ga hukumomin Najeriya a galabaice.”
Tuni kuma da kungiyar lauyoyi ‘yan kabilar Igbo, ta bakin shugabanta Chief Chuks Muomah (SAN), ta yi Allah wadai da kamun na Nnamdi Kanu, wanda ta ce “ya saba doka, a yanayin da aka kama shi aka dawo da shi Najeriya.”
“Muna nan muna kokarin ganin gwamnatin Burtaniya ta shigo domin ta rusa wannan kamun da ya saba doka” in ji Chief Muomah, a yayin tattaunawa da manema labarai a garin Aba.
Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Igbo, Biafra, Biyafara, DSS, IPOB, Abuja, Nigeria, da Najeriya.
Ya kara da cewa “mun kuma ba da takardar gayyata mai wa’adi, domin tattara dukkan manyan lauyoyinmu a duk fadin duniya, domin shirya ingantacciyar kariya a karkashin dokokin kasa da kuma na kasa-da-kasa, domin kare hakkokin Mazi Nnamdi Kanu."
A ranar 26 ga watan nan na Yuli ne za’a soma ci gaba da zaman shara’ar ta Nnamdi Kanu a wata babbar kotun tarayya ta Abuja, inda ake tuhumar sa da laifukan cin amannar kasa, tunzura jama’a da haddasa tashin hankali da ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dukiyoyi da dai sauran tuhume-tuhume.
An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
Your browser doesn’t support HTML5