A sanarwar da suka fitar a ranar Juma’a 20 ga watan Oktoba a karkashin jagorancin Maitre Mohamed Seydou Diagne, wanda ofishinsa ke birnin Dakar, sa’oi kadan bayan da hukumomin mulkin sojan Nijar suka zargi shugaba Mohamed Bazoum da yunkurin tserewa daga inda yake tsare, lauyoyin da ke kare hambararren shugaban kasar ta Nijar sun yi watsi da abin da suka kira tsarin da aka kitsa takanas.
Jagoran wadanan lauyoyi Me Seydou Diagne yace tsare Bazoum a asirce abu ne da ke nunin sojojin da suka yi juyin mulki sun fara fice gona da iri dangane da yadda suke toye mahimman ‘yancin mutunen da suke karewa.
Shi kuwa Me Reed Brody, lauya mai ofishi a birnin New York, ya ayyana cewa suna bukatar hukumomin mulkin sojan Nijar su ba su hujjojin da ke tabbatar da cewa shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa na raye sannan kuma ya zama wajibi su hanzarta sakinsu daga inda suke tsare.
A zargi mutun da yunkurin arcewa alhali ba a hannun mashara’anta yake ba abu ne da hankali ba zai dauka ba, inji Me Reed, ya kara da cewa a maimakon haka kamata ya yi alkali mai shigar da kara Procureur de la Republique ya tuhumi wadanda tun a ranar 26 ga watan Yuli su ke tsare da mutanen da su ke karewa.
Wadannan lauyoyi a wani bangare na sanarwar da suka fitar, sun yi tunatarwa a kan yadda tun a ranar da aka yi juyin mulki wato 26 ga watan Yulin shekarar 2023 a Nijar shugaba Bazoum da matarsa Hadiza da dansu Salem ke tsare a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai, ba a taba gabatar da su gaban wani alkali ba haka kuma ba a taba sanar da su cewa ga abin da ake nufi da su a shari’ance ba.
An katse masu wutar lantarki tun a ranar 2 ga watan Agusta, likita kadai ke da izinin kai masu ziyara ya na kuma kai masu abinci a duk kwana biyu.
A ranar Juma’a 20 ga watan Oktoba da safe an hana likitan shiga ya gansu alhali ya je ne dauke da abinci da ya saba kai masu a cewar wadannan lauyoyi.
Sanarwar ta kuma kara yin tunatar wa a game da karar da hambararren shugaban ya shigar a kotun CEDEAO a ranar 15 ga watan Satumba a bisa bukatar ta dauki mataki kan mahukuntan Nijar saboda tauye masa muhimman hakkoki da ‘yancin gudanar da harkokin siyasa sakamakon hana masa tafiyar da lamuran mulkin kasa kamar yadda aka dora masa nauyin gudanarwa ta hanyar dimokradiyya.
Your browser doesn’t support HTML5