Duk da kokawa da halin kuncin rayuwa, jama'a a jihar Adamawa basu fasa yin abun da suke yi ba lokacin bikin sallah na zuwa gaida sarakuna.
Har yau ana cigaba da bukukuwan sallah inda mutane na tururuwa zuwa gaida manyan sarakuna.
A jawabinsa ga dimbim jama'a da suka taru a fadarsa, Lamidon Adamawa Dr. Barkindo Aliyu Mustapha kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Adamawa yayi tsokaci ne dangane da samun zaman lafiya musamman tsakanin makiyaya da manoma.
Lamidon ya lura da irin mugun tashin hankalin dake faruwa tsakaninsu cikin 'yan kwanakin nan. Yace kullum yana samun rahotannin hasarar dukiyoyi da rayuka saboda rashin kauna, rashin imani da rashin fahimtar juna. Akwai kuma rashin kiyayewa da hakkin dake rataye kan kowa.
Sarkin ya kira jama'a da su hada kai tare da kiran gwamnati ta inganta tsaro da bada goyon baya iya gwargwado domin daukan matakan da suka dace.
Ya nuna farin cikinsa ga gwamnatin Adamawa saboda kebe kadada dubu biyar domin anfanin makiyaya, inda zasu dinga kiwo maimakon shiga gonakan mutane da dabbobinsu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulazi da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5