Sakataren gwamnatin jiha Dr. Umar Bindir ya furta haka a hirarsa da Muryar Amurka lokacin walimar cin abincin bukin babbar Sallah da gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Umaru Jibirilla ya jagoranta a sansanin Malkohi na karamar hukumar Yola ta Kudu.
Da yake bayanin dalilinsa na zabin cin abincin Sallah tare da ‘yan gudun hijira a sansanin maimakon gidan gwamnati, gwamna Muhammadu Umaru Jibirilla ya ce yin haka alama ce ta nuna kaunarsa ga lafiyar ‘yan gudun hijirar domin ya kara tabbatar masu gwamnati na da masaniya da halin da suke ciki.
Gwamnan ya ce duk da cewa sama da kashi saba’in na su ba ‘yan asalin jiha bane, a matsayinsu na ‘yan Najeriya hakkinsa ne ya tabbatar da samar masu da muhimman bukatunsu na yau da kullum. Kana ya jinjinawa kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya keyi wajen dakile ayukan ta’addanci a arewa maso gabashin kasar.
Wasu yara ‘yan gudun hijira da manyansu sun nuna farin ciki da irin karramawa da gwamnan jihar Adamawa ya yi masu.
Karo na farko ke nan da wani gwamna da majalisar zartaswarsa ya shiyar irin wannan walimar tun da kafa sansanonin ranar ashirin da hudu ga watan Agustan dubu biyu da goma sha hudu.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.