Lamarin na Neman Shafan Harkokin Sifiri da Rabon Man Fetur

Bisa ga dukan alamu dai rikicin shugabancin da ya dabaybaye shugabanin hadakar kungiyar dillalen man fetur a Najeriya, na neman komawa rassan kungiyar na jihohi , lamari da yanzu haka ke neman shafan harkokin sifiri da kuma raba man fetur a shiyar Yola.

Shiyar dai ta kunshi jihohin Adamawa da Taraba, inda kungiyoyi biyu ke takaddama game da shugabancin kungiyar, bangaren Alhaji Abubakar Butu ‘yan ta lauye bisa jagorancin Alhaji Dahiru Buba Kaburiye.

Ganin yadda wannan takaddama ke kara safafa yasa uwar kungiyar ta kasa ta turo tawaga ta masamma domin shawo kan lamarin, Alhaji Aminu Adamu, shugaban kungiyar a shiyar arewa maso gabas bayan wani taron siri, ya bukaci ‘yayan kungiyar dasu kai zuciya nesa domin ci gaban kungiyar.