Laifina Ne Da Barcelona Ta Lallasa Mu – Carlo Ancelotti

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti

Wannan shi ne karo na shida a jere da Barcelona take kaucewa shan kaye a wasan na ‘El Clasico.’

Mai horar da ‘yan wasan Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya dora laifin kayen da suka sha hannun abokanan hamayyarsu Barcelona akansa.

A ranar Lahadi Barcelona ta lallasa Madrid da ci 4-0 a wasan hamayya na ‘El Clasico’

Dan wasan Barcelona Pierre- Emerick ya zura kwallaye biyu a wasan, sai kuma Ronald Araujo da Ferran Torres suka saka nasu tukwicin kwallayen.

“Dabarun da na yi amfani da su, ba su da kan gado, ba su ba mu sakamako mai kyau ba. ‘Yan wasan Barca sun taka kwallo fiye da mu, kuma sun cancanci nasarar da suka samu.” In ji Ancelotti kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Wannan shi ne karo na shida a jere da Barcelona take kaucewa shan kaye a wasan na ‘El Clasico.’

Yanzu Barcelona ta haura zuwa mataki na uku, tana kuma da tazarar maki 12 tsakaninta da Real a teburin gasar La Liga.