Dan wasan Paris Saint Germain, Kylian Mbappe ya caccaki kungiyarsa kan yadda suka tafiyar da bukatar da ya mika musu ta cewa yana so ya bar su a watan Yuli.
Real Madrid ta nuna sha’awar sayen dan wasan akan kudi fam miliyan 197 amma PSG ta ki maincewa, duk da cewa kwantiragin dan wasan na shirin karewa a karshen wannan kakar wasa.
Dan shekara 22, Mbappe ya koma kungiyar ta PSG a shekarar 2017 akan kudi fam miliyan 165.
“A gaskiya ban ji dadi ba da suka ce sai a karshen watan Agusta na sanar da su cewa zan tafi, bayan tun a karshen wata Yuli na fada musu cewa ina so na tafi.” Mbappe ya fadawa Rediyon wasannin ta RMC da ke kasar Faransa kamar yadda Sky Sports ya ruwaito.
Ya kara da cewa, “amma duk da haka, PSG kungiya ce da ta fito da ni. Na kasance mai farin ciki a zamana cikin shekaru hudu da na kwashe, kuma har yanzu ina cikin farin ciki.”
Kofunan gasa uku Mbappe ya ciwo wa kungiyar ta PSG a gasra Ligue 1.
Kuma a yanzu haka shi ne dan wasan da ya fi yawan kwallaye a wannan kakar wasa inda yake da kwallo hudu.
Gabanin kalaman na Mbappe, Darektan wasannin kungiyar Leonardo ya fada cewa yana da kwarin gwiwar dan wasan zai sabunta kwantiraginsa da kungiyar.