Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari, yace bai mallaki kamfanin sarrafa man fetur a kasar Malta ba, sannan bai san wani daga cikin jami’an kamfanin daya mallaki irin wannan masana’anta a kasar dake kan tsibiri a nahiyar Turai ba.
A karshen makon daya gabata, Dangote, yace wasu jami’an kamfanin NNPC da dillalan man fetur na gudanar da wata masana’antar sarrafa albarkatun man fetur a Malta, don haka suke kokarin hana tace albarkatun man a gida Najeriya.
A martanin daya mayar a yau Talata, Kyari yace, “domin fayyace zarge-zargen da aka yi game da masana’antar sarrafa albarkatun mai, bana mallaka ko gudanar da kowane irin kasuwanci a ko’ina a fadin duniya kai tsaye ko ta hanyar amfani da wasu in banda gonar da nake nomawa.
"Haka kuma bani da masaniya game da wani jami’in kamfanin NNPC, daya mallaka ko yake gudanar da masana’antar sarrafa albarkatun man a kasar Malta koma wani wuri a duniya.
“Kamfanin tace mai a Malta ko wani bangare na duniya bashi da tasiri akan harkokin kasuwanci ko gudanarwar kamfanin NNPC.”
“Domin kore shakku, zamu yi amfani da dokokinmu na tabbatar da da’a wajen bankado irin wannan jami’i, in akwaishi, kuma ni da kaina zan bada shawarar a fallasa shi tare da mikashi hannun hukumomin tsaro domin daukar matakan da suka dace ”.