Kwaya Da Hodar Iblis Ne Suka Yi Sanadin Mutuwar Mawaki Coolio - Bincike

Coolio Cause of Death

A ranar 28 ga watan Satumbar 2022 mawakin, wanda ya yi fice da wakarsa ta “Gansta’s Paradise” ya rasu a gidansa da ke Los Angele a jihar Califronia.

Masu gudanar da bincike kan mamata a birnin Los Angeles sun ce kwayoyin ‘Fentanyl’ da hodar iblis ne suka yi sanadin mutuwar mawakin Amurka Coolio a bara.

A ranar 28 ga watan Satumbar 2022 mawakin da ya yi fice da wakarsa ta “Gansta’s Paradise” ya rasu a gidansa da ke Los Angele a jihar Califronia.

Bincikensu ya kuma gano cewa Coolio mai shekaru 59 na dauke da wata cuta da ke hana jini ya gudana a sassan jiki.

Kazalika masu binciken sun ce cutar Asthma da yake fama da ita da kuma yawan shan taba da mawakin ke yi, sun taimaka wajen mutuwarsa.

Manajan Coolia Jarez Posey a ranar Alhamis shi ma ya tabbatar da dalilan da suka kai ga mutuwar mawakin wanda ya shahara a shekarun 1990’s