Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu


FILE PHOTO: Lisa Marie Presley
FILE PHOTO: Lisa Marie Presley

Lisa Marie Presley, mawakiya kuma diya daya tilo ga fitaccen mawakin nan Elvis Presley, ta rasu jiya Alhamis bayan da aka garzaya da ita wani asibiti a yankin Los Angeles, kamar yadda mahaifiyarta ta bayyana.

A cikin wata sanarwa da mahaifiyarta Priscilla Presley ta fitar ta ce “cikin alhini ina sanar da ku mummunan labari cewa, kyakkyawar diyata Lisa Marie ta rasu." Lisa Marie tana da shekaru 54 da haihuwa.

Sanarwar ta kara da cewa, “Ita ce macen da tafi nuna kulawa, karfi da soyayya da na taba sani. Muna neman a mutunta kadaicinmu yayin da muke kokarin ji da wannan babban rashi.”

Lisa Marie ta samu bugun zuciya a gidanta da ke Calabasas da ke wajen Los Angeles, a cewar shafin yanar gizo na TMZ. Daga nan aka kai ta asibiti a ranar Alhamis.

FILE - Elvis Presley da matarsa Priscilla da diyarsa Lisa Marie, a daki a asibitin Baptist a Memphis, Tenn., Feb. 5, 1968.
FILE - Elvis Presley da matarsa Priscilla da diyarsa Lisa Marie, a daki a asibitin Baptist a Memphis, Tenn., Feb. 5, 1968.

An haife ta a shekara ta 1968 kuma ita ce ta mallaki kasaitaccen gidan mahaifinta Graceland a Memphis, sanannen wurin yawon bude ido. Tana ‘yar shekara 9 da haihuwa ne Elvis ya mutu a Graceland a 1977.

Ta fara waka a shekarar 2003 da kundin wakoki mai suna “To Whom It May Concern.” A shekarar 2005 ta fito da “Now What,” kuma duka biyun suna kan gaba a cikin fitattun wakoki 10 a jerin kundin wakoki 200 na Billboard.

An fitar da kundin wakokinta na uku mai suna “Storm and Grace,” a cikin 2012.

FILE PHOTO: Michael Jackson da matarsa Lisa Marie Presley-Jackson
FILE PHOTO: Michael Jackson da matarsa Lisa Marie Presley-Jackson

Ta yi aure sau hudu. Ta auri shahararran mawakin nan Michael Jackson, a shekarar 1994, kwanki 20 kacal bayan rabuwarta da mijinta na farko, mawaki Danny Keough.

Aurensu da ya dauki hankali ya mutu a 1996 yayin da Jackson ke fama da zargin lalata da yara.

Presley ta auri jarumi Nicholas Cage, babban mai son mahaifinta, a cikin 2002. Cage ya shigar da kara saki bayan watanni hudu.

Macau Huading Awards
Macau Huading Awards

Ta daura auranta na hudu da mai kada mata garaya kuma mai shirya kida Michael Lockwood. Kuma sun rabu a 2021.

Ta haifi ‘ya’ya hudu. Danta tilo, Benjamin Keough, ya mutu a shekara ta 2020 yana da shekaru 27. Diyarta Riley Keough, jaruma ce mai shekaru 33.

Sauran ‘yayanta mata biyu tagwaye ne Harper da Finley Lockwood, ‘yan shekaru 14.

XS
SM
MD
LG