Javaid Rehman, wakili na musamman mai zaman kansa kan halin da ake ciki a Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya ce ya kamata a hukunta irin wannan babban take hakkin dan Adam, duk da la’akari da lokacin da aka aikata laifin.
Ya kara da cewa, "Kada a bar gwamnatin Iran da shugabanninta su kubuta daga laifukan da suka aikata na cin zarafin bil'adama da kisan kare dangi a kasar."
Yace, Wasu sun bada rahotan cewa, an yi wa mata fyade kafin a kashe su, kuma akwai yara da dama a cikin wadanda aka kashe.
Rehman ya koka da cewa, "An ci gaba da kai hari da cin zarafin 'yan tsiraru na addini, kabilanci da harshe da kuma 'yan adawa na siyasa ba tare da wani hukunci ba a tsawon shekaru goma na farko na kafa Jamhuriyar Musulunci a shekara ta 1979."
Ya yi tsokaci kan hare-haren da ake kaiwa Bahai - mafi yawan marasa rinjaye na Iran - wadanda ba musulmi ba - wanda ya ce "an yi ne da nufin kisan kare dangi da kuma zalunci."
Ba kamar sauran tsiraru ba, kundin tsarin mulkin Iran bai amince da addinin Bahais ba kuma ba su da wakilci a Majalisar dokoki.
Rehman, wanda Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta nada amma ba da yawun Majalisar Dinkin Duniya ya ke magana ba, ya yi nuni da rahotannin cewa, an kashe mabiya addini Bahais fiye da 200 daga farkon shekarun 1980, yayin da aka kama dubbai.
A yayin da Iran ke murkushe kungiyoyin da ke adawa da Musulunci, ya kuma bayar da shawarar cewa, su ma an yi wa masu bin tafarkin Markisanci da zindiqai da sauran mabiya wadansu addinai kisan kiyashi.
Rahoton na Rehman ya kuma yi nuni da kisan gillar da ake yi wa dubban matasa musamman matasa a gidajen yarin Iran a cikin 'yan watanni a lokacin bazara na shekara ta 1988, a daidai lokacin da ake kawo karshen yakin Iran da Iraki, yana mai bayyana hakan a matsayin "labari mai ban tsoro na ta'addanci."
Wadanda aka kashe galibi magoya bayan kungiyar Mujahedin ta Iran ne - kungiyar da Iran ta dauka a matsayin kungiyar ta'addanci da ke goyon bayan Bagadaza a lokacin rikicin.
Masanin ya koka da cewa "gwamnatin Iran tana ci gaba da musanta " aikata laifin ta'addanci," kuma ba a gurfanar da masu aikata laifin gaban kotu ba. Yace "samar da tsarin bincike na kasa da kasa mai zaman kansa a kan Iran yana da matukar muhimmanci."
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi gargadi a baya a cikin watan Afrilu cewa, cin zarafin da hukumomin Iran ke yi wa tsirarun ‘yan Bahai na take hakkin bil'adama ne
Ku Duba Wannan Ma Iran Za Ta Dasa Na’urorin Daukan Hoto Don Kama Matan Da Ba Sa Saka Hijabi