Ali Reza Akbari ya kasance tsohon mataimakin ministan tsaro na Iran, kuma an tuhume shi da laifin yi wa Birtaniya leken asiri.
A ranar Asabar, kamfanin dillancin labarai na Mizan na Iran ya sanar da mutuwar Akbari bayan an rataye shi, amma ba a kai ga bayyana lokacin da aka aiwatar da hukuncin kisan ba. An kama shi a shekarar 2019.
Birtaniya da Amurka sun bukaci Iran da kada ta aiwatar da hukuncin kisa.
Kungiyar Amnesty reshen Iran ta wallafa a shafinta na Twitter cewa rataye Akbari ya nuna "mummunan matakin da hukumomin Iran ke dauka kan hakkin rayuwa. Amfani da hukuncin kisa yana da ban tsoro a kowane irin yanayi."
Firayim Ministan Biritaniya Rishi Sunak ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Wannan mummunan aiki ne da rashin tsoro, wanda gwamnatin dabbanci ta aiwatar ba tare da mutunta hakkin bil'adama na mutanensu ba." Ya ce "ya firgita."
Shi ma sakataren harkokin wajen Birtaniya James Cleverly, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, "Wannan ta'addancin ya cancanci yin Allah wadai da kakkausar murya.
“Tuhumar da aka yi wa Ali Reza Akbari da kuma hukuncin kisan na da nasaba da siyasa.” A cewar mataimakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Vedant Patel a ranar Juma’a kafin a aiwatar da hukuncin. "Mun damu matuka da rahotannin da ke cewa an baiwa wa Mista Akbari miyagun kwayoyi, an azabtar da shi yayin da yake tsare, an yi masa tambayoyi na tsawon dubban sa'o'i, kuma an tilasta masa fadin karya."
A farkon makon nan, BBC Persia ta watsa wani sakon murya daga Akbari. Ya ce an yi masa tambayoyi tare da azabtar da shi “sama da sa’o’i 3,500” kuma an tilasta masa ya amsa laifukan da bai aikata ba.