'Yan Najeriya sun fara muhawara akan mulkin Buhari cikin kwanaki dari da yayi yanzu yana mulki.
Wasu na ganin an samu nasarori yayinda 'yan adawa suka ce su basu gani a kasa ba.
Tun lokacin da yake neman a zabeshi shugaban kasa Muhammad Buhari yayi alwashin yaki da cin hanci da rashawa da kuma magance tabarbarewar tsaro tare da kawar da Boko Haram kungiyar ta'adanci da tayi kamarin suna. Yayi alkawarin samarda wutar lantarki.
To saidai jam'iyyar adawa ta PDP ta nuna rashin gamsuwarta da gwamnatin Buhari musamman akan tattalin arziki. Tana ganin gwamnatin Buhari na lalube ne a duhu tare da cewa hana saka dala a bankuna tsarin mulkin 'yan gurguzu ne.
Jibrin Zakka Jigawa dan PDP ne wanda yace yakamata 'yan Najeriya su ji kanshin gwamnati da kudaden da tace tayi anfani dasu. Kamata yayi gwamnati ta koma kan manoma da 'yan kasuwa yana cewa kada a yi mulki irin na wadancan shekarun.
Ibrahim Abdulkarim darakta na ofishin goyon bayan Buhari yace 'yan watani ba zasu isa a yi alkalanci akan mulkin Buhari ba. Idan za'a yiwa shugaban adalci a bashi shekara daya kana a yi waiwaya.
Duk da haka Ibrahim Abdulkarim yace an samu sauyi domin yadda ake aiki a ma'aikatun gwamnati ya canza. Abubuwan da da ba'a yi yanzu ana yinsu.
Sanata Hadi Sirikia mukarrabin Buhari yace an taso daga inda mutane suka fi karfin doka zuwa inda doka tafi karfin mutane. Da kowa diban abun da ya ga dama yake daga asusun gwamnati saboda suna da yawa amma yanzu asusu ya zama daya tak.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5