Zazzabin da tattalin arzikin Najeriya, yayi ta fama dashi ana daf da kawo karshen milkin shugaba Goodluck Jonathan, ya jefa Gwamnatoci jahohi cikin halin kaka ni kayi Jangwangwamar kuma da sabbin Gwamnoni suka gada a halin yanzu.
Tun a lokaci sai da jahohi kimani goma sha takwas ta kai ko albashi ma basu iya biya, abun yafi Kamari a jahohin Filato da Benue da Osun.
Shugaba Muhammadu Buhari, wanda bai boye bacin ransa ba yace bazai yadda ma’aikaci a lokaci milkinsa ba zai iya samu albashi ba dalilin ke nan da shugaban ya kirkiro da tsarin ceto jahohi da ake kira {Bailout}.
Wani masanin tattalin arziki a Najeriya, Yusha’u Aliyu, yace wannan wani tsarin ne da shugaban kasa cikin karamci aka shigo domin a taimakawa mutanen da suka yiwa Gwamnati aiyuka kuma suka chanchanta a biya su wanda suma suna da wasu hakkoki akansu da kuma bukatun wadanda suke mu’amala dasu, wannan ana taimaki tattalin arziki domin a ceto ma’aikata wadanda aka rike masu hakkokin su.
Dr. Nazifi Abdullahi Darma, na jami’ar Abuja, yace duk wani Gwamna da yake tunanin cewa sai zauna ya dogara da kudin da yake samu daga Gwamnatin tarayya domin ya tafiyarda harkokin jahar sat oh gaskiya wannan lokacin ya shige.
Ya kara da cewa ko da farashin mai ya tashi bukatu na jama’a da yawan jama’a sun karu saboda haka dole tunani na Gwamnoni ya canja daga dogaro da abun da suke samu daga Gwamnatin Tarayya kowa ya duba jahar sa.