Jahar Lagos, dai ta kasance cibiyar hada hadar kasuwancin Afirka, kuma jahar da hukumar Kwastam ke samun akasarin kudaden shigar ta bisa la’akari da tashoshin jiragen ruwa da na sama da kuma kan iyaka da jamhuriyar Benin, da kuma manyan kamfanoni dake jahar ta Lagos.
Hukumar ta Kwastam dai ta kasance ta biyu bayan hukumar NNPC, wajen samarwa Najeriya, kudaden shiga.
Wani mai harkar fiton kayayyaki da tashoshin jiragen ruwa Alhaji Musa Wushishi, ya bayana wa Wakilin muryar Amurka, Babangida Jibrin, cewa tunda kyara aka zo yi toh tabbacin hakika idan ya samu goyon bayan saura mayan jami’an Kwastam to za’a ga canji suma kuma zasu ji dadi.
Suma a bangarensu ma’aikatan hukumar ta Kwastam sun yi mamakin wannan nadi na wani daga wajen hukumar, sai dai sun ce hakan ba sabon abu bane, inda a baya Birgediya Ango, ya taba jagorantar hukumar ta Kwastam.
Wani jami’in Kwastam, da ya nemi a sakaya sunan sa yace sun yi murna da samun sabon shugaba, da fatan samun canji ba kamar wanda ya gada ba saboda basu samun zuwa yin kwasa kwasai sa’ilin na kudaden alawus na makalewa.
Kanar Hameed Ali, murabus wanda ya taba zama tsohon Kantoman jahar Kaduna yayi kaurin suna wajen babu sani ba sabo wajen gudanar da aiyuka bil haki da gaskiya tare kuma da magance matsalar cin hanci da rashawa.
Abun da ake ganin ya kasance daya daga cikin dalilan da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada shi a matsayin shugaba hukumar ta Kwastam.