Kwamitin zaman lafiya na kasar wato NPC ya gudanar da wani muhimmin taro da masu ruwa da tsaki ciki har da ‘yan takara, hukumar zabe ta INEC, da sauran masu ruwa da tsaki don sake jadada mahimmacnin ‘yan takara su gujewa cin mutunci juna don a gudanar da zabe cikin zaman lafiya da lumana.
Kwamitin na NPC ya gudanar da wannan taron ne a birnin tarayya Abuja don yin jan kunne ga ‘yan takara, masu yin magana da yawunsu da kuma magoya bayansu dake amfanin da kalmomi mara dadin ji da su guji ci gaba da yin furuci da ka iya jawo rashin zaman lafiya a lokacin zaben watan Febrairu mai gabatowa da ma bayan zaben ta hanyar bayyana manufofinsu ga masu jefa kuri’a a maimakon yin zage-zage na cin mutuncin juna.
A yayin taron da aka gudanar cikin sirri bayan baiwa 'yan jarida damar shiga na wasu mintuna, an tattauna muhimman batuttuwa da suka jibanci samo mafita ga koke-koken ‘yan takara, yin adalci ga dukkaninsu da kuma tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe ta yadda dukkan ‘yan kasa zasu yi alfahari da shi kamar yadda mamba a kwamitin NPC kuma shugaban gidan talabijan na Channels, Dakta John Momoh ya shaida mana.
Kazalika, a yayin taron an dan sami arangama sakamakon yadda kwamitin ya ki baiwa wasu ‘yan takara dama su yi jawabi saboda rikicin cikin gida da hukuncin kotu da suke kan fama da shi inda aka basu dama da su sasanta tsakaninsu kafin taro na gaba kamar yadda mataimakin dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar tsagin jam’iyyar ADC, Ahmed Buhari ya bayyana.
A nasa bangare, dan takarar jam’iyyar Action Alliance, Dakta Hamza Al-Mustapha, ya yi karin haske a game da yanayin da suke ciki a cikin jam’iyyarsu kuma ya bukaci a yiwa kowa adalci kasancewar maganar rikicin cikin gida ya taso a lokacin taron.
Gudanar da wannan taron dai baya rasa nasaba da irin furuci mara dadin ji da ‘yan takara da magoya bayansu suke yi a yawancin lokacin jawabi idan suka je gangamin yakin neman zabe inda limamin darikar Katolika na jihar Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su guji yin fada da juna a daidai wannan lokaci.
Ita ma kungiyar Compatriots dake da mambobi a duk sassan Najeriya ta bakin mamba, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ta gana da kwamitin zaman lafiya a gefe guda domin nuna goyon bayanta ga aikin kwamitin, tare da yin kira ga shugabbani da su yi kiwon jama’a da abubuwan da zasu fadi da wadanda zasu yi.
Baya ga shugaban kwamitin, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, limamin darikar Katolika na jihar Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, da dai sauransu, taron ya sami halartar ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, na jam’iyyar Action Alliance, Dakta Hamza Al-Mustapha, jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore; mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa, mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Bishop Isaac Idahosa, da dai sauran masu ruwa da tsaki.
Shugaban kwamitin, janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya rufe taron ne da sakon cewa za’a tabbatar da yiwa dukkanin ‘yan takara adalci a lokacin zabe da ma bayan zaben.
Kwamitin dai zai gudanar da taron rattaba hannu a kan yarjejeniya ta karshe kafin a gudanar da zaben a ranar 18 ga watan Febrairu mai zuwa wato kwanaki 7 kacal kafin a gudanar da babban zaben shekarar 2023.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5